27 Afirilu 2022 - 18:47
Za’a Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Kudus A Garuruwa 900 A Fadin Kasar Iran

Da yake ganawa na manema labarai a yau shugaban majalisar ci gaban musulunci na Iran Hojjatul islam Mohammad Hussaini Musapour ya fadi cewa akwai sama da masu daukar hoto guda 5000 tare da yan jarida na cikin gida da waje da za su halarci wajen babban taron zanga-zangar ranar Qudus ta duniya da za’a yi a nan kasar iran aranar juma’a mai zuwa kamar yadda jagoran juyin musulunci na Iran marigayi Imam Khumaini ya assasa.

Yace za’a gudanar da babban taron kan alummar falasdinu da ake zalunta a yankin gaza inda jagororin kungiyoyin gwagwarmaya za su yi jawabai a wajen, kum za’a gudanar da irinsa a gaban tsohon ofishin jakadancin Amurka da ken an birnin Tehran da ake kira da shaker leken Asiri.

Agefe guda kuma ya fadi cewa Isra’ila za ta rushe daga cikin gida ne masana sun yi amanna cewa yanzu ba wai kungiyar Hizbullah da iran ne kawai babbar barazana ga isra’ila ba matsalolin cikin gida dake take fama da su su ne mafi hatsari dake mata barazana.

Daga karshe yace Isra’ila da ta ke takama da karfin soja a yankin amma yanzu tana tangantangal ne na neman rushewa.duk kuwa da irin goyon bayan da take samu daga kasashen Amurka fransa da birtaniya.

342/